Javier Solana zai je birnin Teheran dauke da ihsanin da ak yiwa Iran | Labarai | DW | 05.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Javier Solana zai je birnin Teheran dauke da ihsanin da ak yiwa Iran

Babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana zai kai wata ziyara a birnin Teheran a gobe talata don gabatarwa Iran wani tayin taimako da nufin shawo kanta ta daina shirin ta na sarrafa sinadarin uranium. An jiyo haka ne daga majiyoyin kungyiar EU. An amince da wannan tayin taimako ne a wani taron da ministocin harkokin wajen kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD hade da Jamus suka yi cikin makon jiya a birnin Vienna. Ana kyautata zato wannan tayin dai ya hada da taimako a fannonin cinikaiya, tsaro da kuma fasahohi. An kuma yi barazanar daukar tsauraran matakai kan Iran idan taki yin watsi da shirin ta na nukiliya, wanda kasashen yamma ke gani ta na yi ne don kera makaman kare dangi.