Jarrabawar zama Bajamushe | Zamantakewa | DW | 12.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Jarrabawar zama Bajamushe

An ɓullo da sababbin jerin tambayoyi ga masu sha´awar zama ´yan ƙasar Jamus.

default

Matan Turkawa baki a Berlin

Kuɗin zama ɗan ƙasar Jamus ya kama Euro 255. To amma hanyar kaiwa wannan matsayi na da tsawo. Dole sai mai son zama Bajamushen ya shafe tsawon shekaru takwas a cikin ƙasar ba tare da ya aikata wani laifi ba. Kuma dole ya iya samarwa kansa kuɗin biyan dukkan buƙatunsa na rayuwa tare da naƙaltar dokoki da kuma harshen ƙasar. Sannan daga watan Satumba za a ɓullo da sabuwar jarrabawa ga masu sha´awar zaman ´yan ƙasar ta Jamus. Wannan matakin na shan suka a cikin ƙasar kamar yadda za ku ji ƙarin bayani a cikin wannan rahoto na Mohammad Nasiru Awal.


Daga jerin tambayoyi 33 dole mai sha´awar zama ɗa kasar ta Jamus ya amsa aƙalla kashi 50 cikin 100 daidai. Waɗannan tambayoyi sun shafi fannoni na siyasa, tarihi da kuma zamantakewa a Jamus. Kenan Kolat shugaban ƙungiyar Turkawa a Jamus ya saka ayar tambaya ga wannan jarrabawa.


Kolat ya ce "Mai mutum zai yi, bayan ya shirya yin wannan jarrabawa kuma ya haddace dukkan tambayoyin amma daga baya ya manta da su baki ɗaya? Saboda haka wannan ba zai canza komai ba."


Daga ɓangaren ´yan adawa ana ta da jijiyar wuya dangane da sabuwar jarrabawar, musamman wata tambaya mai ɗaure kai dangane da dalilin da ya sa a shekarar 1970 tsohon shugaban gwamnati Willy Brandt ya durƙusa kan guiwowinsa a wata tsohuwar unguwar Yahudawa marasa galihu dake birnin Warsaw. Ko da yake an ba da jerin amsoshi waɗanda daga ciki za a zaɓi guda, amma mataimakin shugaban ɓangaren jam´iyar The Greens a majalsiar dokoki Hans Christian Ströbele ya yi tsokaci yana mai cewa.


Ströbele: "Na yi imani da yawa daga cikin Jamusawa kansu ba za su iya amsa waɗannan tambayoyi kai tsaye wato kamar dalilin durƙusawar Willy Brandt ba tare da wani bincike mai zurfi ba."


Cibiyar haɓaka ilimi ta jami´ar Humboldt dake birnin Berlin ta tsara waɗannan tambayoyi. Daga cikin tambayoyi dubu ɗaya da cibiyar ta rarrabawa mutane dubu biyar, masana ilimin kimiyya sun zaɓi 310, waɗanda daga cikinsu ake zaɓan 33 a cikin ko wace jarrabawar neman takardun zama Bajamushe.


Ganin cewa tambayoyi ba na neman sanin zurfin ilimin mutum ba ne illa iyaka tantance masaniyarsa ce game da ƙasar ta Jamus, jam´iyar SPD dake cikin gwamnatin ƙawancen ta tarayya ta yi maraba da su. Wani jerin tambayoyi da jihar Hesse ta ɓullo da shi a cikin shekara ta 2006, ya sha suka da kakkausan lafazi domin ya ƙunshi tambayoyi na ƙwaƙwaf da sanin wasu ɗabi´u masu ɗaure kai musamman waɗanda suka shafi addinin musulunci. To sai dai ba a taɓa amfani da waɗannan tambayoyi na jihar ta Hesse ba.


Duk da haka jam´iyar SPD ta na asaka ayar tambaya dangane da sabon jeri tambayoyin na zama ɗan ƙasar ta Jamus. Kakakin ta a majalisar dokoki Dieter Wiefelspütz ya ce da akwai buƙatar zama a tattauna akna wannan batu. Ya ce ya zama wajibi gwamnatin ƙawance ta yi wata zazzafar mahawwara musamman saboda muhimmanci da kuma ɗaure kai na waɗannan tambayoyi.


A bara baƙi dubu 126 suka karɓi takardun zama ´yan ƙasar ta Jamus, wato an samu raguwar kashi ɗaya bisa uku idan aka kwatanta da yawan su a shekara ta 2000.