1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jarin 'yan ƙasuwa na ƙetare a Afirka

October 25, 2010

Nahiyar Afirka na daɗa zama dandalin zuba jari ga 'yan kasuwa na ƙasashen ƙetare saboda bunƙasar tattalin arziƙin da take samu

https://p.dw.com/p/PnoK
Afirka na samun bunƙasar tattalin arziƙiHoto: picture-alliance / Jorn Stjerneklar / Impact Photos

A yau dai zamu fara ne da rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ke batu a game da yiwuwar bunƙasar yawan kuɗaɗen jari da 'yan kasuwa na ƙetare ke zubawa a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce:

"Daidai irin abin dake faruwa a ƙasar Brazil, inda ake samun bunƙasar matasa masu matsakaicin ƙarfin tattalin arziƙi, shi ne ake hangen samuwarsa a nahiyar Afirka. A sakamakon canje-canjen da ake samu a fannoni na tattalin arziƙi da siyasa da zamantakewa za a samu wadata ga jama'a a nahiyar. Ko ba daɗe ko ba jima ba za a bar Afirka a baya ba matsawar da ƙasashen nahiyar suka samu kwanciyar hankali aka kuma kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen dake addabar wasu ƙasashe na Afirka."

To sai dai kuma jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung a lokaci guda ta taɓo mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar Guinea, inda ake fama da tashe-tashen hankula a daidai lokacin da ake shirye-shiryen kaɗa ƙuri'ar raba gardama tsakanin masu takarar zaɓen shugaban ƙasar da suka yi shaura. Ire-Iren waɗannan tashe-tashen hankula da juye-juyen mulki da kuma salon mulkin nan na kama-karya na daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu ga ci gaban nahiyar Afirka...

Brand bei Wahl in Guinea Flash-Galerie
Tashe-tashen hankula kan hana ruwa gudu ga ci gaban AfirkaHoto: AP

A wani mataki na ƙwacen filayen noma, kamar yadda ƙungiyoyin taimako masu zaman kansu suka nunar, jaridar Der Tagesspiegel rahoton dake cewar:

"A sakamakon alƙawarin da aka yi musu na kyautata makomar rayuwarsu, wasu ƙananan manoma a ƙasar Saliyo suka ba filayensu ga wani ɗan kasuwa daga ƙasar Switzerland, wanda ke noman rake da rogo don samar da makamashin nan na Ethol, a yayinda su kuma manoman a maimakon kyautatuwar rayuwarsu suka shiga wani mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi. Wannan sabon makamashin shi ne damenti mai tattare da jini a halin yanzu."

Landraub in Kambodscha
Matsalar ƙwace filayen noma daga ƙananan manomaHoto: Thomas Kruchem

Wani bincike na baya-bayan nan da aka gudanar ya gano cewar 'yan Afirka sai daɗa ƙiba suke yi ba ƙaƙƙautawa, in ji jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce:

"An samu ƙaruwar kashi 35% na yawan masu ƙiba fiye da kima a nahiyar Afirka idan an kwatanta da misalin shekaru ashirin da suka wuce. A sakamakon haka ake samun yawaitar ciwurwuta masu nasaba da ƙibar. Musabbabin haka kuwa shi ne bunƙasar da ake samu ta gidajen abincin nan na fast-food, waɗanda suka barbazu a biranen Afirka da Kudu da Kenya da Nijeriya, inda ya zama wani abin taƙama ne mutun ya tattara iyalinsa su je cin abinci a irin waɗannan wurare, musamman a ƙarshen mako."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal