1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun turai na ta kara buga zanen batanci ga annabi Muhammadu (s.a.w)

February 3, 2006

Jaridun nahiyar Turai, sun ci gaba da buga zanen hotunan nan da ke batanci ga annabi Muhammadu (s.a.w), wadanda wata jaridar kasar Dennmark ta fara bugawa. Jama'a da dama dai sun bayyana bacin ransu da cewa wannan dai danyen aiki ne na tsokana.

https://p.dw.com/p/BvTt
Musulmin kasar Indonesiya na zanga-zanga gaban ofishin jakadancin Dennmark a birnin Jakarta.
Musulmin kasar Indonesiya na zanga-zanga gaban ofishin jakadancin Dennmark a birnin Jakarta.Hoto: AP

Addinin islama dai, ya haramta duk wani salo na siffanta annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ta hanyar zane ko mutum mutumi da dai sauransu. Buga surar wani zanen da jaridar nan Jyllands-Posten ta kasar Dennmark ta yi, wanda ke ßatanci ga annabi Muhammadu, yake nuna shi tamkar dan ta’adda, ta janyo matukar ßacin ran musulmi a duk duniya baki daya. Duk da cewa, a halin yanzu, jaridar ta yi nadamar abin da ta yi, ta kuma nemi gafara, batun bai tsaya nan ba. Wasu jaridun kasashen nahiyar Turai, a cikinsu kuwa har da mujallar nan ta Jamus, wato „Die Welt“, sun sake buga zanen tare hujjanta abin da suka yi da cewa, ai yin amfani ne da `yancinsu na jaridu. Amma kwararrun masana halayen zaman jama’a da na addini sun bayyana cewa, wannan ba kome ba ne illa tsokana, kuma ta tsantsa. Kamar yadda Udo Steinbach, darektan cibiyar nazarin harkokin Gabas Ta Tsakiya da ke birnin Hamburg ya bayyanar:-

„Wannan dai abin ban takaici ne. Kuma ya zo ne a daidai lokacin da ake samun hauhawar tsamari tsakanin wasu yankuna na duniyar musulmi da kasashen Yamma. To a nan dai tambayar da za a iya yi ita ce, ina ne matukar `yancin fadar albarkacin baki ? Wai shin kowa na da `yancin aikata duk abin da ya ga dama ba tare da iyakace haddin abin da yake yi ba ? Idan dai na dubi irin zanen da aka buga, sai in ga cewa aikin marasa hankali ne. Saboda ba zai janyo wata fa’ida ga kowa ba, kuma ba shi da wata daraja ma a ko wace huska. A nawa ganin dai, wannan wato tsokana ce kawai ta tsantsa, kuma abin ban takaici ne buga zanen a wannan lokacin.“

Amma `yan siyasan Jamus dai na bayyana ra’ayi ne daban. Suna ganin duk lamarin ne a huskar `yancin jarida. Ta dogaro kan hakan ne dai jam’iyyun SPD da Greens da FDP suka bayyana cewa yana da muhimmanci kwarai a sami tuntußar juna da mabiya addinin islama.

Manyan kungiyoyin musulmi a nan Jamus dai, musamman ma na Turkawa sun bayyana mamakinsu ga buga jerin zane-zanen a cikin jaridun nan kasar. Duk da hakan dai sun yi kira ga gamayyar Turkawa a nan Jamus da su guji duk wani abin da zai janyo tashe-tashen hankulla. Shugaban gamayyar, Kenan Kolat, ya yi kira ga kafofin yada labaran da su yi la’akari da abin da zai tayar wa musulmi hankali a cikin rahotannin da suke bugawa.

Turkawa da yawa dai sun yi Allah wadai da buga zane-zanen a jaridu. Beyza Bilgin, wata malamar fannin addini a jami’ar Ankara ta kasar Turkiyya, ta ce siffanta annabi Muhammadu tamkar dan ta’adda da aka yi a zanen, ba abu ne da za a iya amincewa da shi ba:-

„Shakka babu, zana surar annabi kuma tamkar dan ta’adda, ai ba bain da kowa ma zai yarda da shi ba ne. Yakin da annabin ya yi ma, ai na wani dan gajeren lokaci ne. A kwanakin bayan na karanta wani littafi cikin turanci, inda aka bayyana cewa, adadin kwanakin da annabi ya yi yaki a duk tsawon rayuwarsa, bai fi wata daya ba. Amma ya dukufad da duk lokacinsa rayuwarsa ne wajen samad da zaman lafiya.“

A gnin Farfesa Abdulaziz Bayindir, shi ma shaihin malamin addini a jami’ar Istanbul:-

„Ai batun ma ba na siffanta annabin ba ne kawai. Wato burin masu zanen ne su yi tsokana. A zahiri, irin wadannan mutanen na ganin kansu ne kamar sun isa su yi halitta. Hakan kuwa, ba wani abin mamaki ba ne, saboda a cikin tarin hadisansa ma, manzo ya ambaci irin wadannan mutanen.“

Ridvan Cakir, shugaban wata kungiyar islama ta Turkawa a nan Jamus, ya gargadi duk musulmi a nan kasar da ma ko’ina da ka da su bari wannan aikin banzan ya tayar musu da hankali, ko ma ya sami wani angizo a kansu. Saboda hakan, ba zai janyo kome ba illa asara ga duk al’ummai.