1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Zaben Somaliya da farin dango a Afirka

Mohammad Nasiru Awal
February 10, 2017

Zaben shugaban kasa a Somaliya da barazanar farin dango da ke cinye amfani gona a Afirka da dakile kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2XLgp
Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Mohamed Abdullahi Farmajo ya zama sabon shugaban SomaliyaHoto: Getty Images/AFP/M. Haji Abdinur

Za mu fara sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung da leka kasar Somaliya tana mai cewa zaben shugaban kasa tsakanin buhuhunan rairayi da kangon gine-gine. Ta ce tsohon Firaminista Mohamed Abdullahi Mohamed da aka fi sani da Farmanjo ya lashe zaben shugaban kasar Somaliya. An gudanar da zaben ne mai sarkakiya a wani bangare na filin jirgin sama karkashin tsauraran matakan tsaro. To sai dai ba zabe ne da al'ummar kasa suka sauke nauyin da ke kansu ba, a'a majalisa ce mai wakilan manyan kabilun kasar suka zabi shugaban a wani tsarin zabe mai daure kai da ya biyo bayan wani yakin neman zabe mai cike da cin hanci da rashawa da bada toshiyar baki.

Barazanar farin dango a Afirka

Heuschrecken in Mauritanien
Hoto: AP

Rundunar farin dango inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa a Afirka wasu fari na barazanar cinye albarkar noma.

Jaridar ta ce kamar rundunar sojoji farin dango da wasu kwari da ba su da abokan gogayya yanzu haka suna bazuwa kamar wutar daji a nahiyar Afirka. Da zarar sun farma gona sai sun ga bayanta. Jaridar ta ruwaito kungiyar abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya na nuna fargabar cewa yanzu haka farin ka iya lalata albarkatun noma da ake sa ran samu a kakar bana a da yawa daga cikin kasashen yammaci da kudancin Afirka.  Abin damuwa ma shi ne farin za su fi yin ta'adi ne a yankunan da a shekarun baya-bayan nan sauyin yanayi na El Nino ya haddasa fari da karancin abinci.

Matakan dakile kwararar bakin haure

Mittelmeer Migranten und Flüchtlinge in Schlauchboot
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Diab

Kasashen Turai sun lashi takobin dakile kwararar bakin haure musamman daga kasashen Afirka kudu da Sahara, inji jaridar Die Tageszeitung.

Ta ce an samu ra'ayi mabambamta a taron koli tsakanin Turai da Afirka a tsibirin Malta dangane da batun na bakin haure. Jaridar ta ce yayin da wasu ke goyon bayan rage yawan bakin haure wasu kuwa na son a kara yawan masu shigowa Turan ta hanyoyin halattattu.  Duk da yabon da suka sha game da yarjejeniyar da suka kulla da Tarayyar Turai, kasashen Afirka biyar da suka hada da Nijar, Najeriya, Senegal, Mali da kuma Habasha, har yanzu Turan na mai ra'ayin cewa ka'idojin yarjejeniyar da suka tanadi ba wa wadannan kasashen karin taimakon raya kasa ba su wadatar ba, Turan na son kasashen Afirka suka kara kaimi a yaki da masu safarar mutane.

Kamaru ta bada mamaki a gasar AFCON

A karshe sai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta yi tsokaci kan nasara lashe kofin kwallon kafar Afirka da Kamaru ta yi tana mai cewa ko da yake wannan shi ne karo na biyar da kungiyar kwallon kafar ta Kamaru ta lashe kofin nahiyar Afirka, amma ana iya cewa ya zo da mamaki domin tun gabanin gasar ba wanda ya yi zaton Kamaru za ta lashe kofin. hankula sun fi karkata kan kasashen Senegal da Cote d'Ivoire da Ghana da kuma Aljeriya.