1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Kasar Burundi ta fice daga kotun ICC

October 21, 2016

Ficewar Burundi daga kotun ICC da tursasa wa 'yan adawa a Habasha da dage zaben Kwango sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2RWse
Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a labarinta mai taken fargabar zama ruwan dare ta yi tsokaci kan matakin da gwamnatin kasar Burundi ta dauka na ficewa daga kotun kasa da kasa ta ICC.

Jaridar ta ce bayan da a makon da ya gabata majalisar dokokin kasar ta Burundi mai fama da rikici ta zartas da kudurin fita daga kotun ta ICC, a wannan makon Shugaba Pierre Nkurunziza ya albarkaci kudurin tare da sanya masa hannu. Dalilin wannan mataki shi ne hukuncin farko da ICC ta yanke game da take hakkin dan Adam a Burundi, lamarin da gwamnati ta kwatanta da yi mata shisshigi maras iyaka cikin harkokinta na cikin gida. Ta zargi ICC da zama wani makami da kasashen yamma ke amfani da ita wajen tauye kasashen Afirka. Tun ba yau ba kasashen Afirka da dama na sukar lamirin kotun da cewa ta nuna wa nahiyar Afirka wariya. Yanzu dai Burundi ta zama kasar farko da ta fice daga ICC.

Tsaurara matakan tauyen 'yancin walwala

Daga Burundi sai kasar Habasha wato Ethiopia inda a labarin da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce har yanzu ana ci gaba da tursasa wa jama'a. Maimakon bude kofofi ga al'umma kamar yadda ta alkawarta, gwamnatin Habasha ta kara tsananta dokokin tauye ‘yancin walwala.

Äthiopien Unruhen
Gangamin neman 'yancin walwala da sahihiyar demokradiyya a HabashaHoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Jaridar ta ce bayan kafa dokar ta-baci a farkon watan nan na Oktoba, a wannan makon gwamnatin Habasha ta takaita ‘yancin walwala da na fadin albarkacin baki, don kawo karshen bore da zanga-zangar neman demokradiyya a yankunan Oromia da Amhara. Dubban mutane ne kuma aka ruwaito an harbe a yankin Oromia kadai. Lamarin ya yi muni ne a farkon watan nan na Oktoba lokacin da ‘yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye da harsashin gaskiya kann al'ummar Oromo lokacin wani biki a garin Bishoftu.

Jinkirta zaben Kwango ya gamu da turjiya

Take-taken Kabila na karya dokokin kasa, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar hankali kan Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango bayan da wani taron wakilan gwamnati da wasu ‘yan adawa ya amince da dage zaben kasar har zuwa shekarar 2018.

Kongo Proteste gegen Joseph Kabila
Boren adawa da shugabancin Joseph KabilaHoto: Reuters/K. Katombe

Jaridar ta ce yanzu haka dai mafi yawan ‘yan adawar kasar sun yi tir da wannan mataki da suka ce dabara ce ta tsawaita wa'adin mulkin Shugaba Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ya kamata ya kare kuma a gudanar da sabon zabe a ranar 19 ga watan Disamba na wannan shekara. ‘Yan adawa sun ce za su ci gaba da nuna turjiya.

Shugaba Buhari da barkwanci kan matarsa

A karshe sai jaridar Der Tagesspiegel wadda ta yi tsokaci kan kalamar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kan matarsa Aisha Buhari bayan sukar da ta yi kan yadda ake tafiyar da gwamnati. Buharin wanda ya ce matarsa a kicin da kuma falo take, ya sha suka daga kungiyoyi musamman ma na mata. Sai dai a wani kokarin yayyafa ma abin ruwa, kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa ta shafin Twitter cewa barkwanci shugaban ya yi, kuma ba ya yi wadannan kalaman ne don ya kaskanta matarsa ba.