Jaridun Jamus: Fasa bututun mai a yankin Niger Delta da ke Najeriya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Fasa bututun mai a yankin Niger Delta da ke Najeriya

Fasa bututun mai a Najeriya da bullar kwayar cutar Zika a Afirka da siyasar Kwango sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Niger Kämpfer

Tsagerun Niger Delta suka yi kaurin suna wajen fasa bututun mai

Za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neues Deutschland wadda a wannan mako ta leka Najeriya tana mai cewa a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ke cika shekara guda da hawa kan mulki, 'yan ta'adda sun sako arzikin man fetir din Najeriya a gaba.

Jaridar ta ce tsagerun kungiyar Niger Delta Avengers sun lashi takobin durkusar da tattalin arzikin Najeriya inda suke kai hare-hare kan bututan man kasar, lamarin da ya haddasa karancin man da kasar samarwa mafi karanci cikin shekaru 20. A cikin wani sako da ta aike wa dukkan kamfanonin hakar mai a yankin Niger Delta, kungiyar ta ce rundunar sojin Najeriya ba za ta iya kare kadarorin kamfanonin ba. Jaridar ta ce Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas ba za ta iya jure wa wata sabuwar hatsaniya musamman daga tsagerun Niger Delta ba, kasancewa hare-haren da suke kai wa bututan man suna janyo wa kasar wadda ta dogara kan arzikin man fetir, mummunan koma-baya abin kuma da ke barazanar kassara tattalin arzikin kasar.

Kwayoyin cutar Zika a gabar tekun Yammacin Afirka

Cutar Zika ta tsallake tekun Atlantika inji jaridar Süddeutsche Zeitung a labarin da ta buga dangane da kwayar cutar Zika da yanzu haka ta kai wasu kasashen Afirka daga kudancin Amirka.

Zika Virusinstitut in Uganda

Dakin binciken kwayoyin cuta a kasar Yuganda

Ta ce a karon farko tun bayan bullar cutar Zika a kudancin Amirka musamman a kasar Brazil a bara, yanzu haka an gano ta a Afirka, inda wani gwajin kwayoyin halitta ya tabbatar da samuwar cutar Zika a tsibirin Cape Verde na kusa da gabar tekun Yammacin Afirka. Jaridar ta ce wannan labarin abin tada hankali ne domin ya nuna karara cewa kwayoyin cutar Zika ba su tsaya a kudancin Amirka kawai ba. Yanzu dai ya zama wajibi kasashen Afirka su yi nazari tare da duba irin hatsarin da ke akwai sannan su zama cikin shirin ko takwana.

Dan adawar Kwango na jinya a Afirka ta Kudu

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, inda ta rawaito cewa jagoran 'yan adawa Moise Katumbi ya bar kasar bayan wani dukan kawo wuka da aka yi masa, abin da ya sa a tilas aka fice da shi daga kasar zuwa Afirka ta Kudu don a duba lafiyarsa.

Moise Katumbi Chapwe Kongo

Moise Katumbi dan adawar Kwango kuma tsohon gwamnan lardin Katanga

Ta ce gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta kawar da babban dan adawarta a cikin gida, har zuwa wani lokaci nan gaba. Jaridar ta ce Moise Katumbi da ke zama dan takarar neman shugabancin kasa karkashin babban kawancen 'yan adawa kuma tsohon gwamnan wani lardi da ake matukar mutunta shi, ya bar bar kasar zuwa Afirka ta Kudu don yi masa jinya. Sannan wani sammacin kame shi na nan yana jiranshi da zarar ya koma Kwango. Gwammati na zarginsa da zama barazana ga tsaron cikin kasar, inda ya dauki Amirkawa sojojin haya. A cikin watan Afrilu an kame Amirkawa da dama masu ba wa dan siyasar shawara kan harkokin tsaro.