1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Ayyukan tarzoma a Yammacin Afirka

Mohammad Nasiru AwalMarch 18, 2016

Hare-haren ta'addancin da aka kai kasar Cote d'Ivoire da matsalar yunwa a wasu kasashen Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1IFsc
Elfenbeinküste Grand Bassam nach dem Anschlag
Hoto: Reuters/L. Gnago

A labarinta mai taken ta'adda a Cote d'Ivoire jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce duniya gaba daya ta yi tir da hare-haren da reshen kungiyar Al-Qaida a yankin Magreb ta kai a kan otel-otel uku da ke a wurin shakatawa na Grand-Bassam da ke wajen birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar Cote d'Ivoire inda akalla mutane 21 suka rasu ciki har da maharan su uku. Jaridar ta ce harin shi ne irinsa na uku mafi muni da aka kai kan wata cibiyar masu yawon shakatawa a Yammacin Afirka tun bayan watan Nuwamban bara, inda wasu 'yan tarzoma suka farma wani otel Mali, sai kuma a watan Janeru inda 'yan ta'adda suka kai hari kan wani otel da wani wurin shan kofi a Burkina Faso, inda suka halaka mutane da dama. Kungiyar AQMI ta dauki alhakin kai dukkan hare-haren.

Bazuwar ayyukan tarzoma a Afirka ta Yamma

Mali Geiselnahme Hotel in Bamako
Hoto: H. Kouyate/AFP/Getty Images

Al-Qaida na kara bazuwa a Yammacin Afirka inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai mayar da hankali kan harin na ranar Lahadi a yankin na Grand-Bassam mai kunshe da wuraren shakatawa inda a kowane karshen mako yake samun kwarara dubban 'yan shakatawa musamman Turawa. Jaridar ta ce kasar da kawo yanzu ba ta fuskanci harin ta'addanci ba, wannan lamarin ya zo ne daidai lokacin da ta fara samun kwanciyar hankalin siyasa da bunkasar tattalin arzikin bayan shekaru na yakin basasa. Kasar dai ita ke kan gaba wajen noman koko a duniya babbar kawar kasar Faransa ce.

Karancin abinci sakamakon rashin kyawon yanayi

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta mayar da hankali ne kan matsalar yunwa a wasu kasashen Afirka duk da faduwar farashin danyun kaya.

Simbabwe Dürre Maisfeld
Hoto: picture alliance/Photoshot

Jaridar ta ce a halin da ake ciki farashin kayan abinci na faduwa a kasuwar duniya amma talaka ba ya gani a kasa. Yanayin El Nino ya janyo karancin kayan abinci a kasashen Afirka Kudu da Sahara, musamman a kasashen Zimbabuwe, Habasha da wasu yankuna na kasar Afirka ta Kudu. Yanayin na El Nino ya janyo kamfar ruwa da fari da karancin albarkacin noma mafi muni cikin shekaru da yawa a kasashen Afirkar na Kudu da Sahara. Saboda haka masana sun yi amanna cewa a bana kasashe irinsu Zimbabuwe da Malawi za su bukaci tallafin abinci mai yawa daga ketare. Jaridar ta ce ko da yake faduwar farashin man fetir ba za ta kawo saukar ruwan sama da ake bukata ba, amma karancin farashin mai din ka iya taimakawa wadannan kasashen su samu rarar kudin da za su iya tinkarar wannan matsala.

Bankuna na janyewa daga Afirka ta Kudu

Bayan bankin Barclays wasu kamfanonin inshora sun sanar da janye harkokinsu daga kasar Afirka ta Kudu inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Ta ce an fara sabon lale a fannin bankunan kasar Afirka ta Kudu, inda yanzu haka kamfanin inshora na kasar Birtaniya wato Old Mutual ya ba da sanarwar bin sahun bankin na Barclays wanda shi ma na Birtaniya ne, inda ya ce zai sayar wa wani bankin Afirka ta Kudu da wani kamfanin inshorar Afirka kadarorinsa.