Jaridar Post tayi min kage inji.. Chiluba | Labarai | DW | 18.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jaridar Post tayi min kage inji.. Chiluba

Tsohon shugaban kasar Zambia, Frederick Chiluba yace a yanzu haka yana nan yana shireye shiryen kai wata jaridar kasar gaban kotu, bisa kage da tayi masa na cewa yana dauke da kwayar cutar HIV.

Tsohon shugaban , wanda a yanzu haka ke kwance a wani asibiti a kasar Africa ta kudu, tuni ya umarci likitocin nasa dasu rabawa kafafen yada labaru na Zambia sakamakon binciken da akayi masa, wanda ke nuni da cewa bashi dauke da wannan kwayar cuta mai haifar da cutar ta kanjamau.

Kakakin tsohon shugaban Emmanuel Mwamba yace, Chiluba ya yanke hukuncin daukar wannan matakin ne don tabbatarwa da yan kasar cewa bashi dauke da wannan cuta ta HIV.

Mr Emmanuel Mwamba yaci gaba da cewa Chiluba, na kwance ne a asibi bisa matsaloli dake tattare da zuciyar sa, wanda a lokacin ne kuma aka gudanar da gwajin cutar ta HIV, inda sakamako yayi nuni da cewa Chiluba bashi dauke da wannan kwayar cuta.

Koda yake Mr Chiluba mai shekaru 62 na kwance a asibiti, a yanzu haka yana fuskantar tuhuma a gaban kuliya bisa cin hanci da rashawa a zamanin mulkin sa na tsawon shekaru 10.

Idan dai za a iya tunawa, a sharhin ta na karshen mako, Jaridar ta Post tace tsohon shugaban na Zambia na dauke da kwayar cutar ta HIV.