JARIDAR DAILY NEWS TA KASAR ZIMBABWE TA SAMU YANCI | Siyasa | DW | 22.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

JARIDAR DAILY NEWS TA KASAR ZIMBABWE TA SAMU YANCI

Hausawa dai kance mahukurci mawadaci,bayan kusan watanni hudu da rufe gidan wata fitacciyar jarida mai suna Daily News da gwamnatin kasar Zimbabwe tayi a kasar, sai gashi kwana daya da janye jamian tsaron da aka jibge a kofar kamfanin jaridar,jaridar ta Daily News ta koma gudanar da aikinta gadan gadan a yau Alhamis.
A cewar kamfanin dillancin labaru na AFP da dama daga cikin mutanen kasar na yin ruge rugen samun kwafin su na jaridar a ranar ta yau domin karantawa kamar yadda suka saba a baya.
A kuwa farkon shafin jaridar,shugaban kamfanin Sam Sipepa Nkomo ya aike da sakon neman ahuwa ga dunbin makarantan jaridar sakamakon wani tsawon lokaci da aka dauka ba,a buga ta,gami da neman ayi hakuri na irin labarin dake tsakiyar shafin jaridar,wanda yace tsohon labari ne,amma an buga shine ba don komai ba sai don a nunawa mutane cewa i lalle jaridar ta dawo daci gaba da aikinta kamar yadda takeyi a baya. Fitar dai sabon bugun jaridar na yau na a matsayin fita ne ta biyu a tun lokacin da aka rufe ta a ranar 24 ga watan satumba na shekarar data gabata.
Bisa kuwa rahotanni da sauka iske mu bangaren gwamnatin kasar ta Zimbabwe ya rufe gidanan jaridar na Daily News ne sakamakon zargin da tayi mata na cewa ita yar amshin shatan jamiyyar adawa ta kasar ce wato MDC.
Bisa hakan ne kuwa a wasu lokatai da daman gaske gwamnatin take bayar da umarni na cafke aditan gidan jaridar wato Geoffrey Nyarota.
Bangaren gwamnatin kasar ta Zimbabwe yace daukar wadan nan matakai data dingi yi a baya nada nasaba ne da hukuncin da babbar kotun kasar ta yanke ne na cewa kamfanin jaridar bashi da cikakkiyar takarda ta shaidar gudanar da aiki daga hukumar kafofin jaridu na kasar.
Jaridar dai ta Daily News ta kasance jaridar da tafi kalubalantar shugaba Robert Mugabe a cikin ire iren rubutun da take bugawa a tun lokacin data fuskanci akwai matsala dangane da harkokin yau da kukllum na kasar ta fannonin rayuwa daban daban ta bil adama Ita dai wan nan jarida ta Daily News na daya daga cikin fitattun jaridu a kasar ta Zimbabwe da mutane sukafi amanna da ita tare da sayanta akan kowace jarida dake kasar.
Ba a da bayan ta kuwa akwai jaridu masu zaman kansu kamar Chronicle da Daily Mirror,a daya hannun kuma da Herald wacce ta gwamnatin kasar ce.
Game kuwa da rikice rikicen siyasa da kasar ta Zimbabwe take fuskanta,a tsakanin bangaren gwamnati bisa shugabancin Mugabe da bangaren yan adawa bisa jagorancin Morgan Tsvangirai,Shugaban kasar Africa ta kudu thabo Mbeki ya fadawa yan jaridu yau alhamis cewa bangaren gwamnatin kasar ya yarda daya koma kann teburin sulhu da daya bangaren don samun wanzuwar zaman lafiya a kasar mai dorewa.
Thabo mbeki yaci gaba da cewa daukar wannan mataki da Robert Mugabe yayi nada nasaba ne da irin tursasawa da kuma matsi kann hakan da yake fuskanta daga cikin gida da kuma wasu kasashe na duniya masu fada aji ne.