Jaridar Daily Mirror ta tona assirin Bush | Labarai | DW | 24.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jaridar Daily Mirror ta tona assirin Bush

Hukumar kare hakin yan jarida ta dunia, ta bukaci shugaba Bush na Amurika ,da Praministan Britania Tony Blair,su yi wa dunia bayyani, a game da assirin da jaridar Daily Mirror ta Britania ta tona, na cewa a shekara bara, Bush ya kudurci dakarun Amurika su yi kaca kaca ,da gidan Talbajan na Aljazira, da ke birnin Doha na kasar Qatar.

A labarin da j ta buga, jaridar ta shaida cewa, Bush tun tuni, ya yanke wannan shawara, amma Tony Blair ya bashi hakuri.

Fadar gwamnatin Amurika ta karyata wannan zargi da tace ba shi da tushe.

Shugaban hukumar kare yan jarida ta dunia ya gayyaci magabatan Amurika da na Britania, da su yi bayani dalla dalla a kan abin da su ka fada da wanda basu fada ba, domin hakan zai taimaka a samu haske cikin al´amarin.

Bayan bayyanar wannan labari, gwamnatin Britania, ta yi kira ga yan jarida kasar, da su ka wallafa, ko suddura daya, daga wannan batu, na karya a cewar ta.