1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan zata hada kai da Turkiya don magance yaduwar murar tsuntsaye

January 10, 2006
https://p.dw.com/p/BvCo

Japan ta ce kofa a bude take wajen hada kai da Turkiya don yaki da yaduwar masassarar tsuntsaye, inji FM Junichiro Koizumi wanda a yau talata ya fara wata ziyarar aiki ta yini 4 a Turkiya. Mun yi musayar ra´ayoyi akan wannan batu, inji FM Koizumi a lokacin wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan. Koizumi ya ce wannan batu ya shafi duniya baki daya, a saboda haka ministocin kiwon lafiya na kasashen biyu zasu shawarta game da ba juna hadin kai don yakar cutar ta murar tsuntsaye. Rahotannin sun tabbatar da cewa mutane 15 ne a Turkiya suka kamu da kwayoyin nau´in zazzabin tsuntsaye na H5N1 mai mummunan hadari ga bil Adama. A ckin makon jiya mutane yara biyu suka mutu dukkan su ´yan gida daya suka mutu a gabashin Turkiya sakamakon nau´in na H5N1. A wani labarin kuma FM Turkiya Recep Erdogan ya ce an shawo kan yaduwar cutar a cikin kasar sannan ana ci-gaba da yiwa mutanen da suka harbu da kwayoyin H5N1 din kuma ba sa cikin wani mummunan hali.