Japan ta bayana janye dakaraun ta daga Irak | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Japan ta bayana janye dakaraun ta daga Irak

Praministan Japon, Junichiro Koizumi, ya yanke shawara kawo ƙarshen zaman dakarun Japon, a ƙasar Irak.

A wani jawabi da ya gabatar yau ,Praministan ya ce ya ɗauki wannan mataki, bayan dogon nazari, da kuma tantanawa, da ɓangarori daban-daban na ƙasa, da ma gwamnatocin Amurika da na Iraƙin.

Kasar ta aika sojoji 600, tun watan janairu na shekara ta 2004, wanda ke jibge a birnin Samawa na jihar Al Mouthanna.

Praministan Koizumi da zai barin karagar mulki a watan Satumber mai zuwa, ya tabbatar da cewa, Japon zata ci gaba da talafawa Iraƙ, ta wasu hanyoyin na daban.

Ta fannin hare hare kuwa, a yau ma rahotani sun ce a ƙalla, mutane 15 sun rasa rayuka, dukan su yan ta´ada, bayan da sojojin Amurika su ka yi masu luguden wuta.

Sannan kuma, an gano gawawakin sojoji 2, na Amurika, da su ka yi ƙasa ku bisa, tun ranar juma´a da ta wuce.