1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan da Sin sun amince matsawa Koriya ta arewa

October 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bugv

Japan da China sun amince su ci gaba da matsawa Koriya ta arewa lamba akan barazanar da tayi na gwajin makaman mukiliya.

Firaministan Japan dake ziyara kasar Sin da takwaransa Hu Jintao sun sake jaddada kudirinsu na tabbatar da cewa Koriya ta arewan bata mallaki nukiliya ba tare kuma da kira da a koma taberun tattaunawa na kasashe 6 akan batun nukiliya na Koriyan.

A Koriya ta arewan a yau ake bikin cikar shekaru 9 da darewar Kim karagar mulkin kasar.

Idan Koriyan ta samu nasarar gudanar da wannan gwaji,zata zamo kasa ta 8 a duniya da ta mallaki makaman nukiliya ta kuma baiyana.