1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

030810 USA Irak Obama

August 3, 2010

Amurka na cigaba da iƙirarin ingantuwar harkokin tsaro a Iraƙi da kewaye

https://p.dw.com/p/Ob9L
Hoto: AP

Shugaba Barack Obama na Amurka ya sake jadadda cewar, zuwa ƙarshen wannan watan dakarun Amurka kimanin dubu 90 zasu janye daga ƙasar Iraki. Dakarun dai zasu cigaba da gudanar da ayyukan horarwa da kuma tallafawa Jami'an tsaron Iraki, kafin su kammala janyewa baki daya daga ƙasar nan da ƙarshen shekara ta 2011.

Shugaba Barack Obama ya sake jaddada tsarin janye dakarun Amurkan daga Iraƙi ne a jawabin da yayi a Atlanta

"Jim kaɗan bayan bayan na hau karagar mulki, na sanar da sanar da sabbin manufofin mu akan Iraki da yadda zamu mayarwa Iraƙi harkokin tafiyar da ƙasarsu. Kuma na jaddada cewar a ranar 31 ga watan Augusta ne, dakarun Amurka za su kammala ayyukansu a Iraƙi. Kuma abunda muke yi ke nan kamar yadda muka yi alkawari."

Daura ga ɗaruruwan tafin 'yan mazan jiya Obama ya gabatar da matakan da za'a bi na tabbatar da wannan manufa

" Ya ce a yanzu haka mun rufe ɗaruruwan sansanoninmu ko kuma mun mikasu ga Iraki. Muna kawar da miliyoyin na'urorimu. Ya zuwa ƙarshen wannan wata, dakarummu kimanin dubu 90 ne zasu kasance a gida, waɗanda suka bar Iraƙi tun bayan da na hau karagar mulki, sama da dubu 90 suka komo gida"

Hakan kuwa ya kasance ne a karkashin gwamnatinsa. Obama yayi fatan cewar da yawa daga cikin Amurka za su ga hakan a matsayin wata nasara a ɓangaren gwamnatinsa.

Anschlag im Irak auf Pilgerstätte Bagdad Juli 2010
Hoto: AP

Yaƙin Irakin dai ana iya cewar koma baya ne ga Amurka. Domin Sojin ƙasar 4,400 suka rasa rayukansu,a yayinda kimanin dubu 32 suka koma gida Amurka da nakasar jiki ko kuma na hankali.

Wannan dai shine sakamakon yaƙin da tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya ƙaddamar akan Iraki a farkon shekara ta 2003, sakamakon zargin tsohon shugaban Iraƙi marigayi Sadam Hussein da mallakar makaman ƙare dangi.

Barack Obama dai a wancan lokacin yana ɗaya daga cikin 'yan majalisar Dottijan Amurkan da suka yi adawa da matakin afkawa Irakin da karfin Soji. Dangane da haka ne bayan ya kasance Shugaban ƙasa ya yi alkawarin gaggauta kawo ƙarshensa.

Shekaru kusan bakwai da rabi da kashe kimanin dalan Amurka biliyan 900 akan yaƙin na Iraƙi, Barack Obama ya bayyana manufofinsa akan ƙasar, na kawo ƙarshen ayyukan dakarun Amurka, tare da bawa Irakawa 'yancinsu na tafiyar da lamuran ƙasarsu yadda suke muradi.

Sai dai kimanin sojojin Amurkan dubu 50 zasu cigaba da kasancewa a Irakin har zuwa karshen shekara ta 2011. Waɗanda zasu kula da rufe sansanoninsu da sauran makamansu, tare da tabbatar da samar da zaman lafiya a ƙasar da manazarta ke bayyana shi da kasancewa tashin hankali da yaƙin basasa.

Kunduz Anschlag
Hoto: AP

Daga cikin masu maraba da wannan mataki na janyewan dakarun Amurkan daga Iraki dai har da Tsohon General Barry McCaffery. Yace hakan shine abu mafi dacewa, duk dacewar kasar na fuskantar kalubale masu yawa.

" yace babu gwamnati. Bisa ga tsario zamu fice daga kasar nan da karshen shekara mai zuwa. Idan har Irakawan basu shirya tafiyar da gwamnati zuwa wannan lokacin ba mai zai faru? Idan har abun ya koma kamar yakin basasa, zai kasance abu mawuyaci mu sake tsoma kammu, domin hakan ba zai dace ba, kasancewar baya bisa tsari".

Sai dai duk da haka shugaba Barack Obama ya kuduri niyyan ficewar Amurka daga Iraki, domin har yanzu akwai lokaci na wanke kai, kuma a yanzu Amurka na ikirarin ingantuwan harkokin tsaro a Iraki da kewaye fiye da lokacin da aka kaddamar da yaƙin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Umaru Aliyu