Janyewar dakarun Amirka daga Iraƙi | Labarai | DW | 19.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janyewar dakarun Amirka daga Iraƙi

Amirka ta fara janye sojojin ta daga Iraƙi kafin cikar wa'adin da ta tsara yin hakan

default

Da safiyar wannan Alhamis ne dakarun Amirka suka fara barin ƙasar Iraƙi kusan makonni biyu gabannin cikar wa'adin da shugaban Amirka Barak Obama ya ajiye. A cewar tashar NBC News, tuni jerin motocin da ke ɗauke da rukunin dakarun suka tsallaka zuwa iyakar ƙasar Kuwait, fiye da shekaru bakwai kenan bayan mamayar da Amirka ta jagoranta wadda kuma ta yi sanadiyyar hamɓarar da tsohon shugaban Iraƙi Saddam Hussein.

Yaƙin da dakarun Amirka ke yi a ƙasar dai - a hukumance, yana cika ne a ranar 31 ga wata Agusta. Kimanin sojoji dubu 50 ne Amirkar za ta kyale a Iraƙi har zuwa ƙarshen shekara mai zuwa. Ficewar dakarun yana zuwa ne yini ɗaya kachal bayan wani ɗan harin ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a wata cibiyar horar da kuratan sojojin Iraƙi dake birnin Bagadaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 59.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu