Janar Petraeus ya isa a birnin Kaboul
July 2, 2010Talla
Sabon Kwamandan rundunar tsaro ta dakarun ƙasa da ƙasa a Afganistan janar Petraeus ya isa a birnin Kaboul. Janar Petraeus wanda zai ɗauki shugabancin rundunar tsaron ta ISAF mai dakaru dubu goma shahuɗu dake yaƙi da 'yan ƙungiyar Taliban, an shirya zai bayyana a karon farko a gaban jama'a a gobe Asabar a birnin Kaboul inda aka shirya wani biki a ofishin jakadancin Amurka.
Ya zuwa yanzu dai tun farkon wannan shekara sojojin ƙawance kimanin 325 suka rasa rayukansu a cikin faɗa da dakarun na ƙasa da ƙasa suke gobzawa da 'yan Taliban.
A makon jiya ne dai shugaba Barack Obama ya naɗa Janar Petreaus akan muƙamin bayan marabus na tsofon shugaban rudunar.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal