Janar Nkunda a gabashin Kongo ya janye daga shirin tsagaita wuta | Labarai | DW | 08.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janar Nkunda a gabashin Kongo ya janye daga shirin tsagaita wuta

Madugun ´yan tawaye na kabilar Tutsi a gabashin JDK Janar Laurent Nkunda ya ba da sanarwar janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta ´yar tsawon wata guda. Janar din ya kuma zargi sojojin gwamnati da kai hari akan arewacin lardin Kivu. Janar Nkunda ya ce ´yan tawayen sa zasu kaddamar da hare hare akan dakarun gwamnati. Tun a ranar alhamis da ta gabata sabon fada ya barke kuma har yanzu ana ci-gaba da gwabzawa a yankin Virunga. Yanzu haka dai ana nuna damuwa game da sabbin tashe tashen hankula da zasu jefa rayuwa mutane cikin mawuyacin hali a lardin na Kivu dake arewa maso gabashin Kongo. A farkon watan satumba dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD suka shiga tsakani akan cimma shirin tsagaita wuta.