Janar Gusau ya yi murabus | Labarai | DW | 19.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janar Gusau ya yi murabus

Mai baiwa shugaban Najeria shawara kan tsaro Aliyu Gusau ya yi murabus, a wani abinda ke nuna yadda siyasar Najeriya za ta kasance a zaɓen baɗi

default

Goodluck Jonathan

A dai dai lokacin da siyasar Najeriya ke ƙara zafafa yau mai bai shugaban ƙasar shawara kan harkar tsaro janar Aliyu Gusau ya yi murabus, inda rohotonni suka ce ya yi hakan ne domin ya samu damar tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen baɗi. Hakan na nufin zai ƙalubalanci shugaba Jonathan wanda ya ƙaddamar da kampen na yin tarace a jiya. Wani na hannun daman janaral Gusau yace tun a ranar Alhamis janar ɗin ya miƙa takardar murabus ga shugaba Goodluck Jonathan, kana ranar Juma'a sai ya shaidawa shubana cewa shi ma zai shiga takarar shugabancin ƙasar. Wannan dai ya ƙara tabbatar da labarin da aka watsa na cewa, wasu gaggan 'yan arewacin Najeriya sun amince su goyi bayan mutun guda a zaɓen baɗi, mutanen da suka haɗa da tsohon shugaban ƙasar Janar Babangida, tsohon mataimakin shugaba Atiku Abubakar da Gwamnan jahar Kwara Boukola Saraki, da shi kansa janar Aliyu Gusau duk sun shimma yarjejeniyar marawa mutum guda baya. Jonathan dake riƙe da madafun iko yana fiskantar ƙalubale cikin jam'iyarsa bisa tsarin karɓa-karɓa, dake rubuce a kuddin tsarin mulkin jam'iyar ta PDP.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu