Jana´izar Serge Maheshe a DRC | Labarai | DW | 15.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jana´izar Serge Maheshe a DRC

Dubun dubunan jama´a, a yankin Bukavu na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo, su ka halarci jana´izar Serge Maheshe, ɗan jaridar nan, na Radio Okapi da wasu yan bindiga su ka hallaka har lahira, ranar laraba da ta wuce.

Radio da ke samun tallafi daga Majalisar Dinkin Dunia, da kuma gidauniyar Hirondelles ta ƙasar Swizland, ta shahara ta fannin waye kann jama´a, a game da al´ammura daban-daban na rayuwa.

Kazalika ta taka rawar gani, a yunƙurin cimma zaman lahia a Jamhuriya Demokradiyar Kongo.

Ƙungiyar yan jarida ta ƙasa da ƙasa wato Reporters sans Frontieres, ta yi Allah wadai ga wannan kisa, ta kuma buƙaci hukumomin Kinshassa, su ɗauki matakin da ya dace, domin binciko masu alhakin wannan aika-aika.