1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janaizar Sadam a Tikrit

December 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuVz

An gudanar da janaizar tsohon shugaban kasar Iraki Sadam Hussein a mahaifarsa dake garin Awja,kusa da Tikrit a yankin arewacin kasar Iraki.An yi wannan jaizar ne da asubahin yau,wanda yazo kasa da saoi 24 bayan zartar da hukuncin kisa akansa jiya da sanyin safiya.Idan zaa iya zunawa ,a shekarata ta 2003 ne kuma aka binne yayansa Sadam maza guda biyu,watau Uday da Qusay a garin na Awja,bayan gamuwa da ajalinsu a fafatawa da dakarun Amurka.A watan daya gabata nedai kotun dake sauraron shariar tsohon shugaban Irakin mai shekaru 69 da haihuwa,ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ,adangane da samunsa da hannun a kisan gilla da akayiwa shiawa 150 a garin Dujail.Gabannin zzartar da wannan hukunci na kisa akan Sadam jiya dai,an dauki tsauraran matakai na tsaro asassa daban daban na Iraki,saboda gudun karin tashe tashen hankula.