Jana′izar Paparoma John Paul na biyu | Siyasa | DW | 08.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jana'izar Paparoma John Paul na biyu

A yau juma'a ne aka yi jana'izar Paparoma John Paul na biyu a dandalin St.Peters dake birnin Rom

Jana'izar Paparoma

Jana'izar Paparoma

Daga cikin manyan jami’an da suka shaidar da jana’izar har da sakatare-janar na MDD Kofi Annan da shugaban kasar Amurka George W. Bush da shuagabannin kasashen Jamus da Faransa da na kasashen Larabawa da kuma nahiyarmu ta Afurka. Kazalika an samu wakilan mujami’un gabacin Turai da kuma na kasashen da basa bin addinin kirista, da suka halarci jana’izar kamar dai shugaba Khatami na kasar iran. A sakamakon haka ake batu a game da wata jana’iza mafi girma da ba a taba ganin irin shigenta ba a cikin tarihi. Marigayi Paparoma John Paul na biyu, shi ne na farko da yayi amfani da kafofdin yada labarai domin daga martabar manufofin diplomasiyyar fadar mulki ta Vatikan a idanun duniya. Mutuwarsa ta taimaka wajen fahimtar da duniya, musamman ma mabiya darikar katolika tasirin da kafofin yada labarai ke da shi a zamantakewa ta yau da kullum, fiye ma da yadda ake zato. Rahotanni masu nasaba da kafar dillancin labaran Vatikan sun ce mutane miliyan daya ne kawai suka zarce zuwa birnin Rom a yau juma’a domin halartar jana’izar, bisa sabanin mutane miliyan hudu da aka yi zato da farko. Bisa ga dukkan alamu kuwa mahukuntan tsaro na kasar italiya ne suka dauki matakai domin kayyade yawan mutanen da za a basu kafar halartar jana’izar a dandalin St. Peters dake birnin Rom. Kazalika mai yiwuwa mummunan yanayin da aka fuskanta ya taimaka wajen kayyade yawan mahalarta dandalin na St. Peters. Saboda an fuskanci kadawar iska mai karfin gaske a duk fadin birnin Rom a yau juma’a, sai kuma bakin hadari da ya dabaibaye samaniyar birnin. Amma abin sha’awa shi ne halin sanin ya kamata a wadannan dimbim mutane suka nunar, suna masu biyayya ga ka’idojin da mahukunta suka shimfida musu, kuma kome ya tafi salin alin ba tare da tangarda ba. Bayan zaman ibadar da aka yi an sake dauke gawar Paparoma John Paul na biyu zuwa mujami’ar St.Peters, inda aka binne gawar tasa, a kabarin tsofon Paparoma John na 23, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo canje-canje ga darikar katolika a cikin karni na 20.