Jana′izar Lech Kaczynski da mai ɗakinsa Maria | Labarai | DW | 18.04.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jana'izar Lech Kaczynski da mai ɗakinsa Maria

An gudanar da jana'iza shugaban ƙasar Poland da matarsa

default

Gawar shugaban ƙasar Poland

An gudanar da jana'izar ban girma ga  shugaban ƙasar Poland Lech Kaczynski da mai ɗakinsa Maria a wata majami'ar da ke a  Cracovie,inda aka ajiye gawarsu naɗe da tutar ƙasar mai launin ja da fari, kafin daga bisanin a kaisu a kushewarsu ta Vavele a bine a kusa da mayan sarakuna da gorzaye na ƙasar.

Mutane sun kai kamar dubu hamsin waɗanda suka ka yi kallon jana'izar ta mayan telbijon da  a ka ajiye a harabar majami ar da aka gudanar da jana'izar, yayin da wasu dubu arba'in ke cikin tsawaran. Da dama daga cikin shugabannin ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da shugabannin ƙasahen Jamus, Amurka,Faransa dakuma Ingila basu samu damar halartaba,saboda gajumarai na toka da su ka mamaye sararin samaniyar Turai a sakamakon tsaunin dake aman wuta a ƙasar Ayisela, abinda ya kawo tsaiko ga harakokin zirga zirga na jiragen sama.Shugaban ƙasar Tchikoslovakiya Vaclav Klaus ya yi kakausar suka dangane da rashin halarta wakilai daga ƙungiyar Tarayya turai a jana'izar wace ta samu halarta  shugabannin ƙasahen Rasha, Hongrie, Yukren, da Romaniya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Yahouza   Sadissou Madobi

 • Kwanan wata 18.04.2010
 • Mawallafi Sadissou Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Mzl1
 • Kwanan wata 18.04.2010
 • Mawallafi Sadissou Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Mzl1