Jana′iza a Duisburg | Labarai | DW | 31.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jana'iza a Duisburg

An yi bankwana da mutanen da suka rasu a hatsarin Love Parade a birnin Duisburg

default

Bishop Franz-Josef Overbeck na birnin Essen yana kunna kyandar, shi ya jagoranci jana'izar da aka yi a birnin Duisburg ta mutanen da suka rasa rayukansu a bikin Love Parade

Mako guda bayan turereniyar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a bikin kiɗa na masoya da ake kira Love Parade a birnin Duisburg na nan Jamus, a yau dubban mutane sun yi bankwana da waɗanda suka mutun. A jana'izar da aka yi a cocin Salvator dake birnin na Duisburg, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban ƙasa Christian Wulff na daga cikin manyan baƙin da suka halarta. Sai kuma masu makoki kimanin 550 ciki har da mutane 100 'yan'uwan waɗanda suka rigamu gidan gaskiyar da kuma jami'an kwana-kwana. A cikin wani gajeren jawabi da ta yi, Firimiyar jihar North Rhein Westfaliya, Hannelore Kraft ta tabbatarwa 'yan'uwan mamatan cewa za a gaggauta gudanar da bincike.

"Shin yaya hakan ta faru? Wane ne ke da laifi, kuma alhakin wa ye? Dole ne mu samo amsoshin waɗannan tambayoyi nan ba da jimawa ba."

An dai nuna bikin addu'o'in kai tsaye akan manyan akwatunan telebijin da aka kakkafa a cikin birnin. To sai dai magajin garin Duisburg Adolf Sauerland bai halarci wurin jana'izar ba saboda dalilai na tsaron lafiyarsa musamman dangane da sukar da yake sha da kuma kiraye kiraye da yayi murabus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar