Janaízar Milosevic a Belgrade | Labarai | DW | 18.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janaízar Milosevic a Belgrade

A kasar Sabiya dubban jamaá ne suka hallara a birnin Belgrade domin yin bankwana da marigayi tsohon shugaban kasar Slobodan Milosevic wanda ake binne shi a yau, mako guda bayan rasuwar sa, a gidan wakafi inda yake fuskantar tuhumar laifukan yaki a kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya dake birnin Hague. Zaá binne gawar Milosevic ne a kauyen su dake Pozarevac mai tazarar kilomita 60 kudu da garin Belgrade, babban birnin kasar Sabiya. A waje guda kuma masu fafutukar cigaban dimokradiyya sun kudiri aniyar gudanar da nasu taron gangamin daura da janaízar, domin nunawa duniya cewa Milosevic ba wani gwarzo ba ne da ya cancanci karramawa. Milosevic ya yi kaurin suna a lokacin yakin Balkans, a tsakanin shekarun 1990 inda mutane kimanin 150,000 suka rasa rayukan su, wasu miliyoyin jamaár kuma suka yi gudun hijira daga kasar.