1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jan Egeland ya gana da shugaban Adawan Uganda

November 12, 2006
https://p.dw.com/p/BucO

Jamiin kula da harkokin tallafi na gaggawa na Mdd Jan Egeland, ya gana da Shugaban kungiyar adawa mafi mugun hali na Uganda watau LRA,Joseph Kony na gajeren lokaci ayau.Ganawar tasu ta gudana ne a garin Ri-Kwagba dake kusa da kann iyakokin Sudan da janmhuriyar democradiyyar Congo.Jakadan na MDD ya nemi yin kira ne ga shugaban kungiyar yan adawan da kotun mdd ke nema ruwa a jallo,dangane da zarginsa da laififfukan gallazawa jamaa azaba,daya saki mata da yara ,wadanda ke tsare a kurkukun kungiyar yan adawan,amma tattaunawar bangarorin biyu ya gaza cimma daidaituwa.Dubban daruruwan mutane suka rasa rayukansu ,ayayinda wasu kimanin million 2 suka rasa matsuggunensu a fadan sheru 20 a yankin arewacin Ugandan,tsakanin kungiyar yan adawa ta LRA da da dakarun gwamnatin shugaba Yoweri museveni.