1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus:Yawan baki da ke zaune a kasar ya karu

Abdullahi Tanko Bala AH
April 20, 2018

Sabbin alkaluma da ofishin kididdigar jama'a na tarayyar Jamus ta fitar ya nuna yawan baki da ke zaune a kasar ya karu da kimanin kashi 5.8 cikin dari a shekarar 2017.

https://p.dw.com/p/2wQH3
Deutschland Berlin Demonstration zu Familiennachzug
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Zuwa karshen 2017 dai a cewar alkaluman kididdigar an yi rajistar baki miliyan goma da dubu dari shida wadanda suka shigo kasar, wanda ya nuna an sami karin mutane 585, 000 ko kuma kashi 5.8 cikin dari idan aka kwatanta da alkaluman shekarar da ta gabata.Tun daga shekarar ta 2015 dai batun 'yan gudun hijira da 'yan cirani ya kasance jigo a jadawalin kungiyar tarayyar Turai da kasashe mambobinta. An dora babban fata da buri mai yawa a kan manufar tallafi ga 'yan gudun hijirar da ke son su koma kasashensu na asali.Wannan manufa dai na tafiya ne kafada da kafada da alkaluman 'yan gudun hijirar da yanayin kasa.

Shin ko wadanne bukatu ne na walwala da siyasa da tattalin arziki suka shafi manufofin ketare na kungiyar tarayyar Turai kan batun 'yan gudun hijirar a kasashen Afirka.? David Kipp masanin kimiyyar siyasa ne a cibiyar nazarin siyasa da tsaro ta kasa da kasa da ke nan Jamus kuma daya daga cikin wadanda suka wallafa wannan rahoto. "Ya ce a wannan nazari mun duba kasashe daban-daban kuma mun duba tasirin kasashen.'' Sabbin alkaluman sun nuna cewar yayin da aka sami raguwar kwararar 'yan gudun hijira a hannu guda 'yan cirani daga kasashen gabashin Turai na karuwa.