1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Toshe iyakoki ba mafita ba ce ga matsalar 'yan gudun hijira

Kamaluddeen SaniJanuary 19, 2016

Ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Frank -Walter Steinmeier ya bayyana cewar toshe kan iyakokin kasashen dake cikin kungiyar tarayyar Turai ba zai iya kaiwa ga magance matsalolin 'yan gudun hijira ba.

https://p.dw.com/p/1Hfyc
Frank-Walter Steinmeier OSCE Rede Wien Österreich
Hoto: picture-alliance/dpa/Ch. Bruna

Frank-Walter Steinmeier yace toshe kan iyakokin ba ita ce maslahar magance batun kwarar 'yan gudun hijira zuwa kasar da tarayyar turai ba.

Mnistan harkokin wajen Jamus din dai na wadan nan kalaman ne a yayin mayar da martani kan jawabin ministan harkokin sufurin Jamus a bisa yun kurin kasar wajen fara shirin toshe kan iyakokin ta.

Kazalika Frank-Walter Steinmeier ya kara da cewar ya zama waji bi a magance yakin basasar Syriya gami da yin aiki tare da makwaftan kasar don takaita yawan kwararar 'yan gudun hijira tare da daukar irin wadan nan matakan a kasashen Girka da Italiya.