Jamusawa sun nuna alhini ga rashin Hans-Dietrich Genscher | Siyasa | DW | 01.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamusawa sun nuna alhini ga rashin Hans-Dietrich Genscher

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Hans-Dietrich Genscher wanda ya rasu ya na da shekaru 89. Shugabannin siyasa na tarayyar Jamus sun nuna ban girma a gareshi.

"Mun zo ne domin mu shaida muku cewa a yau an amince ku tafi." Wadannan kalaman da suka fito daga bakin Hans-Dietrich Genscher za su kasance abin da za a rika tunawa da shi. Ya yi su ne kuwa a ranar 30 ga watan Satumban 1989 a kan benen ginin ofishin jakadancin Jamus ta Yamma da ke birnin Prag. Sai dai ba a ji karshen jawabin ba saboda sowa daga dubun dubaan 'yan Jamus ta Gabas da suka tsere daga kasarsu suka kuma kafa sansani a harabar ofishin jakadancin suna jiran mahukuntan Jamus ta Yamma sun bayyana musu makomarsu. Wannan dai ya kasance wani abin da ya fi sosa masa rai a rayuwarsa ta siyasa, inji Genscher. Sannan sai ya kara da cewa:

"Hakika wannan abu ya fi sosa min rai a tsawon aiki na siyasa. Na fahimci damuwarsu domin ni kaina na tsere daga Jamus ta Gabas sanda neke da yawan shekaru irin na su. Irin sowa ta murna da farin ciki da suka yi bayan na fada musu cewa an bude hanya, ba zan iya kwatanta yadda na ji a zuciya ta ba."

Vertragsunterzeichnung zur Deutschen Einheit in Moskau 1990

Genscher ya taimaka wajen sake hadewar Jamus

A tsawon rayuwarsa dai Hans-Dietrich Genscher ya rike mukaman siyasa da yawa amma ba wanda ya fi taka rawa a rayuwarsa da ya kai na ministan harkokin waje. Ya yi ta balaguro a matsayin babban jami'in diplomasiyya. Bai kuma taba nuna gajiyawa ba a kokarinsa na neman hanyoyin sulhu lokacin yakin cacar baka. Tun a 1974 wasu ke masa lakabi da lauyan adalci tsakanin Gabaci da Yammaci.

'Yan siyasa sun yaba rawar da Genscher ya taka a Jamus

Shugabannin kasar ta Jamus sun nuna alhini tare kuma da nuna ban girma da tsohon ministan harkokin wanda ya rasu da tsakan daren ranar Alhamis yana da shekaru 89 da haihuwa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba masa a matsayin babban dan kishin nahiyar Turai. Shi kuma shugaban kasa Joachim Gauch ya ce Genscher ya fito da Jamus a idanun duniya saboda kwarewarsa da kuma iya aiki a matsayin jami'in diplomasiya.

Galerie Hans-Dietrich Genscher

Genscher ya zama abin misali ga 'yan siyasa a Jamus

Shi kuwa ministan harkokin wajen Jamus na yanzu Frank-Walter Steinmeier cewa ya yi. "Hans-Dietrich Genscher ya taka muhimmiyar rawa a tarihin Jamus da na Turai. Ba wanda ya fi shi dadewa a mukamin ministan harkokin waje wanda ya sadaukar da kansa don kawo karshen raba kasar Jamus da dinke baraka a Turai. A yau mun rasa wani gwarzon dan Jamus kuma dan Turai. Ta'aziyaa ta ga iyalansa baki daya."

A shekarar 1927 aka haifi Genscher a kusa da garin Halle a gabacin Jamus. Bayan karatun jami'a a fannin aikin lauya ya shiga jam'iyyar ra'ayin sassauci kuma ya shaida shekarun farko nam mulkin kwaminisanci a Jamus ta Gabas. A 1952 ya yi kaura zuwa birnin Bremen na arewacin Jamus inad ya yi aiki a matsyin lauya kuma ya shiga jam'iyyar FDP da kuma ya yi wa jagoranci tsawon shekaru 11. Daga 1969 zuwa 1974 ya rike mukamin ministan cikin gida, daga bisani an bashi mukamin ministan harkokin waje tsawon shekaru 18.