Jamus zata taimakawa wajen gina kasar Iraqi | Labarai | DW | 11.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus zata taimakawa wajen gina kasar Iraqi

Mahukuntan Jamus sun sanar da matakin taimakawa Amurka a kokarin da take na kara gina kasar Iraqi bayan yaki.

A cewar kakakin gwamnatin kasar, wato Thomas Steg, mahukuntan na Jamus na shirin fadada horon da dakarun sojin kasar ke bawa jami´an yan sandan kasar ta iraqi.

Bugu da kari, akwai kuma shirin kara yawan kudaden tallafi ga Mdd don ci gaba da bawa matasa horo na koyon sana´oi a kasar ta Iraqi.

Ana sa dai ran tabbatar da wannan shiri daga bakin shugabar gwamnati Angela Merkel a lokacin ganawar su ta keke da keke da shugaba Bush da ake sa ran yi a jibi Juma´a.