1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus zata taimakawa sojin Najeriya

A gobe Alhamis ne ofishin jakadancin Jamus dake Najeriya, zai miƙa taimakon motoci 13 ga rundunar sojin ƙasar.Za´a miƙa taimakon ne a madadin gwamnatin ta Jamus,ta hannun jakadanta dake Najeriya, Mr Joachim Schmillen. Ana sa ran gudanar da bikin miƙa tallafinne, a cibiyar soji dake Magadishu a birnin Abuja ne.Motocin dai sun haɗar da manya da kuma ƙananane, da za´a iya amfani dasu wajen bada horo da kuma ayyukan kiyaye zaman lafiya.An dai ƙiyasta cewa kuɗin motocin ya tasamma Yuro dubu 580.Jamus dai ta daɗe tana taimakawa Najeriya, da irin wannan tallafi, a ɓangarori da daman gaske.