1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata taimaka ga shirin yin sulhu tsakanin Isra´ila da Falasdinawa

December 4, 2006
https://p.dw.com/p/BuZB

Gwamnatin tarayyar Jamus ta yiwa sassan dake rikici da juna a yankin GTT tayin taimako a kokarin cimma zaman lafiya mai dorewa a yankin. A tattaunawar da ya yi lokacin ziyarar sa a Birnin Kudus ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier ya ce Jamus zata taimaka a gudanar da shawarwari kai tsaye tsakanin Israi´ila da Falasdinawa, idan ta karbi ragamar shugabancin KTT a farkon sabuwar shekara. A lokaci daya ministan ya nuna kyakyawan fatan cewa za´a fadada yarjejeniyar tsagaita wuta ta Zirin Gazazuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan. A matakai na karshe na rangadin da yake kaiwa yankin na GTT, a yau ministan zai sauka Syria inda aka shirya zai gana da takwaransa na kasar Walid al-Mullem da kuma shugaban kasa Bashar al-Assad.