Jamus zata karfafa hadin kai da kasashen Afirka | Labarai | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus zata karfafa hadin kai da kasashen Afirka

Gwamnatin tarayyar Jamus ta ce zata karfafa hadin kai da kasashern Afirka idan ta karbi shugabancin KTT da ta G-8 a farkon sabuwar shekara. Ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieckzorek Zeul ta nunar a birnin Berlin cewa Afirka zata zama zakaran gwajin dafi na samun nasarar yakin da ake yi da talauci a duniya baki daya. Ministar ta ce batu mafi muhimmanci shi ne yaki da cutar AIDS ko Sida da kuma taimakawa shirin samar da makamashi mai dorewa. Wani batun kuma shi ne na inganta huldar cinikaiya da raya kasa ta hanyar kulla yarjeniyoyin tattalin arziki, wadanda ake shirin yi tsakanin EU da wasu kasashe matalauta guda 78 kafin karshen shekara mai zuwa.