1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata karbi jagorancin kungiyyar EU

December 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuWa

Shugaban hukumar zartaswa na kungiyyar tarayyar turai, wato Jose Manuel Borroso yace yana cike da fatan za´a cimma nasarori da daman gaske ,a lokacin jagorancin kungiyyar da kasar Jamus zata yi.

Mr Borroso, yaci gaba da cewa akwai kyakkyawan fatan cewa a lokacin wannan mulki na Jamus, shugaba Angela Merkel zata taimaka wajen ganin kwalliya ta biya kudun sabulu, game da burirrikan da kungiyyar ta sa a gaba.

A dai ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekara ne kasar ta Jamus, take karbar ragamar jagorancin kungiyyar ta Eu na karba karba na tsawon watanni shida masu zuwa.