1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata ci gaba da taimakon Uganda da Ruanda

June 4, 2013

Ministan taimakon raya kasashen ketare na Jamus, Dirk Niebel ya kammala ziyara a Afirka ta gabas tare da alkawarin ci gaba da tallafawa kasashen da ya kaiwa ziyara.

https://p.dw.com/p/18jUE
Hoto: picture-alliance/dpa

Duk da nuna damuwa game da rashin kiyaye hakkin yan Adam da cin rashawa, amma ministan taimakon raya kasashen ketare na Jamus, Dirk Niebel yace kasrsa ba zata yi watsi da kasashen Uganda da Ruanda ba. Lokacin ziyara a wadannan kasshe biyu, Niebel yace a maimakon haka ma, Jamus zata ci gaba da basu taimako a fannin bunkasar tattalin arziki da kula da kasafin kudaden jama'a.

Ranar Talata minista Niebel ya kare ziyarar tasa a kasashen na Uganda da Ruanda. Ziyarar a yankin Afirka ta gabas da ministan, dan jam'iyar Free Democrats ya kai, tazo ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Jamus da Uganda take cikin wani hali na wahala. Watanni shidda kafin wannan ziyara, Niebel ya dakatar da kudaden da Jamus ta saba zubawa domin taimakawa kasafin kudin kasar ta Uganda, saboda zargin kasar da laifin cin rashawa da kuma goyon bayan yan tawaye a makwabciyar kasar Jamhuriyar Democradiyar Congo, abin da ya sabawa dokokin duniya. Kazalika, tauye hakkin yan luwadi a kasar ta Uganda, ya taka muhimmiyar rawa a game da kudirin Niebel na dakatar da taimako ga kasar ta Uganda. A shekara ta 2012, kasar ta gabatar da dokar hukuncin kisa ga yan luwadi, ko da shike sakamakon matsin lamba daga kasashe da kungiyoyin duniya, dokar yanzu an dakatar da ita.

To sai dai ko da shike Niebel a lokacin ziyara a Uganda ya kwatanta kasar a matsayin abokiyar hadin gwiwa mai muhimmanci a Afirka ta gabas, ya kuma yabawa ci gaban da take samu a fannin kyautata jin dadn zaman jama'a, hakan ba yana nufin al'amura sun daidaita kenan tsakanin kasashen biyu ba. Lokacin da yake ganawa da wakilan gwamnati a Kampala, Niebel yace:

Uganda Hetzkampagne gegen Homosexuelle Zeitung stellt Schwule an den Pranger
Kampe na adawa da yan luwadi a UgandaHoto: AP

"Yana da muhimmanci kasar ta kiyaye dukkanin matakai na kare hakkin yan Adam. Hakan kuwa ya hada har da yancin kafofin yada labarai da yancin taruka da yancin fadin albarkacin baki da kare hakkin tsiraru. Idan Uganda din ta bullo da sabbin dokokin da zasu rika hukunta masu dabi'ar luwadi, hakan zai sabawa dokokin kasa da kasa".

Duk da haka, Uganda din zata ci gaba da samun taimakon kudi daga Jamus. Daga yanzu zua shekaru ukku masu zuwa, kasar zata sami taimakon misalin Euro miliyan 120, kamar yadda ministan ya nunar a karshen shawarwarinsa a babban birnin kasar.

A karshen ziyarar sa a Kampala, Niebel ya zarce zuwa Ruanda, kasar da a bara Jamus da sauran kasashen kungiyar hadin kan Turai suka dakatar da taimako gaba daya gareta. Binciken Majalisar Dinkin Duniya tun da farko ya nuna cewar Ruanda din ta taimakawa yan tawayen gabashin Congo, yan kungiyar M23, a gwagwarmayar neman kayar da gwamnatin kasar, ko da shike Ruanda din ta musunta wannan zargi. A watan Fabrairu, ma'aikatar taimakon raya kasa ta yanke kudirin maida kudaden taimakon ya zuwa rance na aiyukan raya kasa, ko da shike kungiyar Human Rights Watch tayi korafin rashin dacewar hakan, saboda duk wani mataki na sassautawa Ruandan taimako, kasar tana iya kallonsa a matsayin goyon baya ga manufofinta. Dangane da haka, ministan raya jihohi na Ruanda, James Musoni yace:

Unterzeichnung Friedensabkommen im Kongo
Shugaban kasar Ruanda, Paul KagameHoto: Reuters

"A karshe dai kasashen da suka dora mana takunkumi sun gane gaskiya sun kuma kawar mana da wannan takunkumi. Jamus ta share hanya, ta kuma ja hankalin sauran kasashe su bi sahu, suyi koyi da ita".

Jamus din tayi alkawarin ci gaba da baiwa kasar ta Ruanda taimako, inda kashin farko na Euro miliyan bakwai za'a bayar dashi domin agazawa kasafin kudin kasar na shekara ta 2013 zuwa 2014.

Mawallafi: Sander/Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh