1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus zata ci-gaba da taikakawa Afghanistan duk da kashe sojojinta guda 3

Ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung ya ce dakarun kasarsa zasu ci-gaba da aiki a Afghanistan duk da mutuwar sojojin kasar su 3 a wani harin kunar bakin wake a jiya asabar. A lokacin da yake magana a garin Potsdam, Jung ya ce harin ba zai sa Jamus ta daina taimakawa gwamnatin Afghanistan da kuma al´umar kasar wajen sake gina kasar su ba.

“Kamata yayi mu kara karfafa guiwar sojojin mu amma ba fara wata muhawwara game da janye dakarun mu daga Afghanistan ba.”

Sojojin Jamus guda 3 da farar hular Afghanistan su 6 suka mutu sannan sojoji 5 da mai yi musu tafinta suka jikata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a jikinsa a wata kasuwa dake garin Kunduz a arewacin Afghanistan. ´Yan tawayen Taliban sun yi ikirarin kai harin.