Jamus: Zaben ′yan majalisa a jihar Saarland | Labarai | DW | 26.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Zaben 'yan majalisa a jihar Saarland

A wannan Lahadin ne ake gudanar da zaben 'yan majalisar jihohi na Saarland da ke Kudu maso yammacin Jamus, yankin da ke makwabtaka da kasar Faransa, inda 'yan jihar dubu 800 za su sabunta wakillansu na jiha.

Sai dai wannan zabe ana kallonsa a matsayin zakaran gwajin dafi musamman ga Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, yayin da watanni shida suka rage ga babban zaben kasar, inda jam'iyyarta ta CDU ke fuskantar barazana daga abokiyar kawancenta ta SPD tun bayan da tsohon shugaban majalisar Tarayar Turai Martin Schulz ya sanar da aniyarsa ta neman shugabancin gwamnatin ta Jamus.

Sai dai a wannan yanki da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ke da karfi, binciken jin ra'ayin jama'a ya nunar cewa kashi 35 zuwa 37 cikin 100 na masu zaben na goyon bayan wannan jam'iyya, yayin da binciken ya nunar cewa jam'iyyar SPD za ta iya samun kashi 32 zuwa 34 cikin 100 na masu zaben.