Jamus: Zaben Steinmeier a matsayin shugaban kasa | Labarai | DW | 12.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Zaben Steinmeier a matsayin shugaban kasa

A wannan Lahadin ce ake zaben tsohon ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, a matsayin shugaban kasa wanda zai canji Shugaba Joachim Gauck.

Joachim Gauck und Frank-Walter Steinmeier (picture alliance/dpa/dpa-Zentralbild/B. Pedersen)

Shugaban kasar Jamus mai barin gado Joachim Gauck, tare da Frank-Walter Steinmeier.

Shi dai matsayin shugaban kasa a Jamus na da martaba sosai, amma kuma dukannin karfin ikon ya na a hannun shugaban gwamnati da kuma majalisar dokoki. 'Yan majalisun kasar ne dai da suka hada da na Tarayya da kuma na jihohi da yawansu ya kai mutun 1.260 ne za su yi zaben da tsakiyar wannan rana ta Lahadi. Sai dai tuni kafofin yada labarai ke nuna Steinmeier a matsayin wani mai adawa da Shugaban Amirka Donald Trump bayan da ya sha sukan manufofin sabon shugaban na Amirka.

Dan shekaru 61 da haihuwa Frank-Walter Steinmeier, na da tabbacin samun wannan kujera ta shugabancin kasar ta Jamus, ganin ya na da goyon bayan jam'iyyarsa ta SPD, da kuma jam'iyyar CDU ta Shugabar gwamnati Angela Merkel wadanda su ne jam'iyyun kawancen da ke mulki a kasar ta Jamus.