Jamus za ta wasu matasa daga kasarta | Labarai | DW | 22.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta wasu matasa daga kasarta

Gwamnatin Jamus za ta kori wasu mutane haifaffun kasar da ake zarginsu da zama mata hadari zuwa kasashen iyayensu.

A ranar Talata ne gwamnatin Jamus ta bayyana cewa za ta tasa keyar wasu matasa biyu zuwa kasashen iyayensu, duk da cewar haifaffun Jamus din ne, saboda zarginsu da kitsa hare-hare. Daga ciki matasan dai akwai wani dan Najeriya mai shekaru 22 da kuma wani dan Aljeriya mai shekaru 27, wadanda aka kama a ranar 9 ga watan jiya a tsakiyar birnin Gottingen.

Wannan dai shi ne karo na farko da Jamus ke daukar irin wannan mataki, musamman alakar hakan da kasar haihuwa. Kasar ta Jamus dai ta fuskanci wasu hare-haren ta'addanci cikin watannin baya, ciki har da wanda wani dan kasar Tunisiya ya yi amfani da wata motar dakon kaya, ya tattake mutane a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin, ya kuma kasha rayuka 12.