1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tura dakaru 1.200 zuwa Lebanon.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul1

Gwamnatin Jamus ta ce mai yiwuwa ta ba da gudummowar dakaru fiye da dubu da ɗari biyu ga rundunar kare zaman lafiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta girke a Lebanon. Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ne ya bayyana haka, yayin da yake amsa tambayoyin mamenan labarai yau a birnin Berlin, kafin tashinsa zuwa lardin Kosovo. Ya ƙara da cewa, Jamus za ta tura jiragen ruwan yaƙi tare da jiragen saman hango nesa don hana yin sumogan makamai zuwa ga ƙungiyar Hizbullahi, bayan yaƙin da ta gwabza da Isra’ila. A halin yanzu dai, inji ministan, ana tattaunawa da gwamnatin Lebanon a kan yawan dakarun da Jamus za ta tura, wanda ma zai iya zarce adadin dubu da ɗari biyun da aka yarje a kansa da farko. Duk da hakan dai, mahukuntan birnin Berlin sun ƙi tura dakarun igwa, saboda mai yiwuwa su kara da dakarun Isra’ila, abin da zai iya janyo wata taɓargaza, saboda dalilan tarihi da ke da jiɓinta da mulkin Nazi a Jamus.