1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta janye dakaru daga Turkiya

June 6, 2017

Takaddama da ke tsakanin Jamus da Turkiya ta janyo za a janye sojojin Jamus da ke wani sansani na Turkiya duk da yake kasashen biyu usna kungiyar tsaron NATO.

https://p.dw.com/p/2e9zj
Türkei Incirlik Tornados der Bundeswehr Luftwaffe
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Jamus za ta dauke sojojinta daga sasaninsu mai mahimmancin dake Turkiya izuwa kasar Jodan, hakan dai ya biyo bayan da Turkiya ta ki barin 'yan majalisar dokokin Jamus su kai ziyara wa sojojin. Ministar tsaro Ursula von der Leyen ta ce sojojin Jamus 280 da yanzu haka ke sansanin Incjiirlik da ke kudancin Turkiya, bisa ga alamu za su koma kasar Jodan. Ita dai kasar Turkiya ta kare matsiyin hana 'yan majalisar dokokin kai ziyara, inda ta ce Berlin na ba da mafakar siyasa ga Turkawa da ke da hannun a juyin mulkin da bai nasara ba a bara.

A halin da aka ciki Turkiya ta sanar da soke takardun zama dan kasa ga mutane 130, ciki har da mazaunin kasar Amirka Fethullah Gulen, wanda ake tuhuma da kitsa juyin mulkin da mai nasara ba. Gwamatin Turkiya, ta ce mutanen da aka wallafa sunayensu a jaridu, kodai su dawo kasar su fuskanci shari'a ko kuma soke takardunsu na zama 'yan kasa. 'Yan majalisar dokoki biyu daga bangaren Kurdawa Faysal Sariyildiz da Tugba Hezer Ozturk, suna cikin  jer da aka wallafa.