Jamus za ta hukunta sojoji wadanda suka aikata rashin daá | Labarai | DW | 25.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta hukunta sojoji wadanda suka aikata rashin daá

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin daukar tsauraran matakan hukunci bayan da wata jarida ta buga hotunan wasu sojojin Jamus dauke da kokon kai na wani dan Afghanistan din da aka kashe. Kakakin gwamnatin Thomas Steg yace shugabar gwamnatin ta baiyana matukar damuwar ta da wadannan hotuna marasa kyaun gani. Maáikatar tsaron Jamus ta ce a halin da ake ciki ana tuhumar wasu kuratan sojoji biyu a game da hotunan wadanda ake kyautata tsamanin an dauka a kusa da wani katon rami da aka binne mutane masu yawa a kusa da garin Kabul a shekarar 2003. An buga hotunan ne yau a wata jarida wadda ke fitiowa kowace rana. Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung yace ko kusa ba zaá lamunta da irin wannan danyen aikin da sojojin suka aikata ba.