Jamus za ta fadada ayyukanta zuwa Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jamus za ta fadada ayyukanta zuwa Afirka

Wannan mako mai karewa ya kasance makon Jamus a kasashen Afirka, bisa la'akari da ziyarar shugabar gwamnatin Jamus da ministan harkokin wajen kasar a wasu kasashen Afirka.

A wani sharhi da ta rubuta mai taken "ziyarar kasashe uku, cikin tsukin kwanaki uku, Angela Merkel ta kai ziyarar karfafa kwarin gwiwa tare da ilimantar da masu tserewa daga kasashensu na asali zuwa Turai domin neman tudun mun tsira" jaridar Die Tageszeitung, ta ce Merkel ta yi balaguron gaggawa daga Mali zuwa Yamai sai Ethiopia.

Shugabar gwamnatin ta dukufa ka'in da na'in wajen ziyarar gani da ido don sanin dalilin da ya sa mutane ke barin matsugunnensu na asali zuwa Jamus. Ziyarar da ke zuwa a daidai lokacin da gwamnatin Merkel ke fuskantar matsin lamba daga cikin gida dangane da manufofinta na karbar 'yan gudun hijira. 

 

Ta sha nunar da cewar akwai bukatar kasashen Turai su yaki wannan matsala daga tushe, don ta nan ne kadai za'a iya shawo kan kwararar bakin hauren da ke cigaba da yin dandazo a nahiyar ta Turai. Sai dai akan me mutane zasu dogara, ta yadda ba zasu ji kwadayin fadawa wannan balaguro mai hatsari ba?

A takaice dai a wannan karon ziyarar ta Merkel bai ta'allaka a kan tattalin arziki ba,  sai dai samar da kayayyakin more rayuwa, tsarin shige da fice da batutuwan tsaro.  Idan mutane suna da madogara basu da dalilin tafiya nesa domin neman ingantacciyar rayuwa.

Akwai rarrabuwar kawuna dai tsakanin kasashen na Turai dangane da daukar nauyin 'yan gudun hijira, inda a nan Jamus fushin al'umma na cigaba da karkata kan bakaken fata 'yan Afirka.

 

Ita kuwa jaridar die Welt bude wani sharhi ta yi da cewar, shin wa ke muradin tafiya Afirka na kwana daya ya dawo washe gari? Misali zuwa Abuja fadar gwamnatin Najeriya. Ko shakka babu ba wanda ke muradin haka.

Ziyarar da Frank Walter Steinmeier dai na da burin ganin Najeriya taka rawa wajen tsaida matasanta daga doguwar tafiyar mai hatsari da kuma kan kare da asarar rayuka. Daura da haka, Jamus din ta aiyanna aniyarta na taimakawa batu na tattalin arzikin Najeriyar dake tangal tangal da ma yakar taádancin da kasar ke fama da shi.

 

Zanga-zangar daliban jami'oi a kasar Afirka ta kudu ya dauki hankali jaridun na Jamus a wannan makon. Inda jaridar Die Tageszeitung ta ce, karin kudaden makarantun kasar ya kawo cikas a harkokin koyarwa a makarantun. Gwamnatin Afirka ta kudun dai ta sanar da karin kudaden jami'oin  wanda yawancin dalibai bakaken fata na kasar ba zasu samu sukunin biya ba.

A jami'ar Witwatersrand da ke birnin Johannesburg dai an yi ta dauki ba dadi tsakanin daliban da jami'an 'yan sanda. A cewar jaridar, abun da ya fara daga zanga-zangar dalibai dangane da karin kudin makaranta ya rikide zuwa bore na kan tituna.

A ranar Laraba dai sai da jami'an tsaro a birin Pretoria suka yi ta harbi a iska tare da na hayaki mai sa hawaye, a wani mataki na tarwatsa daliban da suka yi jerin gwano a kan tituna. Adai dai lokacin da daliban ke kukan tsadar karatu ministan ilimi Blade Nzimande, ya sanar da karin kudin a shekarata 2017. A yanzu haka dai dalibai na biyan tsakanin euro 2,000 zuwa 3,800 , banda dakunan kwana da kayan karatu a jami'oin na Afirka ta Kudu.