1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kokarin bunkasa arewacin Nijar

Salissou Boukari
October 11, 2016

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da ta kai ziyara a Jamhuriyar Nijar, ta ce Jamus za ta ware wasu kudade na Euro miliyan 27 domin tallafa wa kasar bisa fannin tsaro, da bunkasa yankin jihar Agadez.

https://p.dw.com/p/2R6IG
Afrika Kanzlerin Merkel besucht Niger
Hoto: Reuters/T. Djibo

Merkel ta ce a shekara daga mai zuwa Jamus za ta zuba miliyan 10 na Euro kan abun da ya shafi samar da kayayakin aikin sojoji, sannan kuma ta ce Jamus na taka rawa a cikin wannan tsari da aka yi wa suna EUCAP mai bada dama wajen horas da jami'an tsaro na 'yan sanda a yakin da ake da 'yan jihadi, sannan kuma ta ce Jamus ta yi alkawarin zuba wasu kudaden Euro miliyan 17 domin bunkasa yankin jihar Agadez a wani mataki na shayo kan matsalar kwararar bakin haure, da kuma munnan safara da ake fuskanta.

Shugaban kasar ta Nijar dai Issoufou Mahamadou ya yaba matakin na Jamus na kafa wata cibiya soja a Nijar domin kula da kayayakin aikin na sojojin da ke ayyukan samar da zaman lafiya a yankin kasar Mali, sannan kuma ya yaba kasancewa sojojin Jamus cikin rundunar MINISMA a yakin da ake da 'yan jihadi kasar ta Mali.