1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta bai wa sojojin Tunusiya horo

Gazali Abdou Tasawa February 21, 2016

Kasar Jamus ta sanar da cewa tana nazarin hanyar aikawa da sojojinta kasar Tunusiya domin bayar da horo ga sojojin wannan kasa dama na makwabciyarta ta Libiya domin su iya fuskantar kalubalan Kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/1HzYA
Bundeswehr Fallschirmjäger Übung
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Zwilling

Kasar Jamus ta sanar da cewa tana nazarin hanyar aikawa da sojojinta a kasar Tunusiya domin bayar da horo ga sojojin wannan kasa dama na makwabciyarta ta Libiya domin su iya fuskantar kalubalan Kungiyar IS wacce sannu a hankali ke samun gidin zama a kasar ta Libiya wanda kuma hakan ke kasancewa babbar barazana ga zaman lafiyar yankin.

Jaridar Bild am Sonntag ta kasar ta Jamus mai fito ko wani mako ta ruwaito cewa ministan harakokin wajen kasar ta Jamus da takwaransa na tsaro za su isa a kasar ta Tunusiya a ranar Alhamis mai zuwa domin nazarin yadda sojojin kasar ta Jamus za su iya aiwatar da wannan shiri nasu.