Jamus: ′Yancin jarida ba abin jinga ba ne | Labarai | DW | 30.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: 'Yancin jarida ba abin jinga ba ne

A lokacin da take kare matakin watsa wani faifayen bidiyon barkwaci ga shugaban Turkiyya Recep Erdogan, Jamus ta ce ba za a sadaukar da 'yancin 'yan jarida ba.

Gwamnatin tarayyar Jamus ta goyi bayan wani faifayen bidiyo na barkwanci ga shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da aka watsa a kafofin watsa labaran Jamus, bayan kakkausar suka daga gwamnatin Turkiyya. Wata mai magana da yawun gwamnatin Jamus a birnin Berlin ta ce irin wadannan shirye-shiryen kafafan yada labaru na daga cikin 'yancin aikin jarida a fagen yada labarun Jamus. Watsa wannan faifayen barkwancin a kan Erdogan da wata tashar telebijin din Jamus ta yi, ya sa mahukunta a birnin Ankara sun gayyaci jakadan Jamus a kasar zuwa ma'aikatar harkokin waje don bayyana masa fushinsu. Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar wajen Jamus a birnin Berlin ta ce jakada Martin Erdmann ya fada wa mahukuntan na Turkiyya cewa Jamus kasa ce da ke mutunta 'yancin 'yan jarida da na fadin albarkacin baki. Faifayen bidiyon dai na shagube ne kan yawaitar daure 'yan jarida a kurkuku, da kuma yadda Turkiyya ta tashi tsaye don ruguza 'yan tawayen Kurdawa a maimakon ta yaki da kungiyar ta'addanci ta IS.