1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Yan sanda na neman wani dan Tunisiya.

Masu bincike a kasar Jamus na neman wani dan kasar Tunisiya, wanda aka samu daya daga cikin takardunsa a cikin babbar motar da aka yi amfani da ita wajen kai hari a kasuwar Kirismati ta birnin Berlin.

Wasu jaridu biyu ne na kasar Jamus, da suka hada da jaridar Bild da kuma Allgemeine Zeitung ne suka sanar da wannan labari, inda suka ce mutumin da ake nema an san shi da sunaye wajen uku, kuma yana da takardar shaidar shekarun haihuwa daban-daban har uku. Ita kuma jaridar der Spiegel mai fitowa a kowane mako a kasar ta Jamus, cewa ta yi wanda ake neman dan asalin birnin Tataouine ne da ke Kudancin kasar ta Tunisiya. Ministan cikin gidan kasar ta Jamus Thomas de Maiziere ya tabbatar da wannan labari yayin wani taron manema labarai, inda ya ce tuni suka gabatar da takardar sammaci a fadin kasar ta jamus da kuma sauran kasashen Turai.

Masu ayyukan binciken sun samu takardun mutumin ne a karkashin kujerar babbar motar da aka yi amfani da ita wajen kai wannan hari. Da yammacin Talata ne dai kungiyar 'yan jihadi ta IS ta dauki alhakin kai harin, da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 12 tare da jikkata wasu da dama.