Jamus: Wani matashi ya kutsa da mota cikin jama′a | Labarai | DW | 26.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Wani matashi ya kutsa da mota cikin jama'a

da yammaci jiya Asabar ne, wani mutun dauke da mota ya kutsa tsakar jama'a a birnin Heidelberg da ke Kudu maso yammacin Jamus, inda ya yi sanadiyyar mutuwar wani dattijo bajamushe mai shekaru 73.

Matashin da ke cikin motar dan kasar Jamus ne mai shekaru 35 da haihuwa inda  kuma ya yi sanadiyyar jikkata wasu mutanen biyu a cewar majiya ta 'yan sanda. Sai dai kuma 'yan sandan sun ce babu wasu alamu da za a iya danganta wannan lamari da aikin ta'addanci.

Da farko dai matashin ya ruga da gudu na niyar tserewa, kafin daga bisani wasu jami'an tsaro su buda masa wuta daf da wurin da hadarin ya afku, inda ya samu mumunan rauni. Tuni dai an yi ma shi tiyata bayan harbin da ya samu, sai dai a cewar jaridar Bild ta nan Jamus mai fitowa a kowace rana, matshin na da matsalar tabin hankali, amma kuma hukumomin tsaron na Jamus ba su kai ga bada wani bayani kan wannan batu ba.

Tun dai bayan harin ta'addancin da wani dan kasar Tunisiya ya kai da wata babbar mota a tsakiya jama'a a birnin Berlin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu da dama ne, hukumomin kasar ta Jamus ke cigaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana dangane da ayyukan 'yan ta'adda a kasar.