1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Tisa keyar 'yan Afghanistan gida

Abdourahamane Hassane
May 31, 2017

Jamus na kokarin sake tisa keyar wasu bakin haure da suka fito daga Afghanistan zuwa gida,sai dai a halin yanzu gwamnatin ta dakatar da tashin wani jirgin dauke da 'yan Afghanistan zuwa gida

https://p.dw.com/p/2dvML
Sabon hari a Afghanistan a dai-dai lokacin da Jamus ke mayar da 'yan kasar da ke neman mafaka
Sabon hari a Afghanistan a dai-dai lokacin da Jamus ke mayar da 'yan kasar da ke neman mafakaHoto: REUTERS/O. Sobhani

Gwamnatin ta Jamus da kuma ta Afghanistan dai sun cimma wata yarjejeniya ta sake mayar da 'yan kasar da ke zaune a Jamus ba bisa kaida ba gida. To sai dai rahoton sabon harin da aka kai kusa da ofisoshin jakadancin wasu kasashen ketare ciki kuwa ha da Jamus din a Afghanistan din, ya sanya Jamus din ta dakatar da mayar da 'yan Afghanistan din da ke neman mafaka a kasar gida. Ko da yake tuni aka mayar da ba'arin wasu 'yan Afghanistan din zuwa gida, kamar Rahmat da ke zaman dan asilin kasar Afghanistan din da ke da shekaru 23 a duniya, wanda ya kasance cikin wadanda batun komen ya rutsa da su. Rahmat dai ya bar kasar sa tun a shekara ta 2011 zuwa Turai, inda da farko ya bi ta kasashen Iran da Turkiya da Italiya da Girka da kuma Faransa kafin daga bisani ya isa Jamus, inda ya zauna a kusa da birnin Stuttgart,  ya ce yana jin tsoro domin kuwa bai san abin da zai faru da shi ba.#b#

Watsi da bukatar samun mafaka

Daga watan Janairu zuwa watan Afrilun da suka gabata ne dai, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Jamus, ta yi watsi da bukatar neman mafaka daga 'yan kasar ta Afghanistan kusan 32,000, kuma Rahmat na daga cikin mutanen 34 da jirgin farko daga Jamus ya daga da su a ranar 14 ga watan Disamba na shekara ta 2016 da ta gabata daga filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Frankfurt, inda ya kai su Kabul babban birnin kasar ta Afghanistan. Tun daga wannan lokaci Jamus din ta ci gaba da mayar da wasu matasa 'yan Afghanistan din zuwa gida wanda a karshen watan Afrilun da ya gabata aka mayar da mutane 107. Fareshta Qedeez jigo ce a wata kungiya da ke sake karbar bakin hauran da aka mayar gida Afghanistan daga Jamus wato IPSO ta ce misali irin na Rahmat zai zame musu wani kalubale na sake iya yin rayuwa a Afghaistan. A halin da ake ciki dai Afghanistan din tana cikin wani mawuyacin hali na rashin tsaro, wanda gwamnatin take da iko da kaso 60 cikin 100 na yankunan kasar yayin da sauran ke hannun dakarun Taliban da wasu kungiyoyin 'yan tawaye kusan guda 20 da ake da su a kasar da ta fada cikin wni hali tun bayan da aka janye sojojin kasa da kasa kusan 10,000, amma dai a yanzu Amirka da NATO na shirin sake tura dakarunsu domin sake dai-daita al'amura.