1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tayi tayin mika taimako ga Syria

Ministar raya kasashe ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul tayiwa kasar syria tayin euro miliyan 4 domin inganta halin rayuwar yan gudun hijira na Iraqi su miliyan daya da dubu dari hudu da suke zaune a kasar.Wieczorek-Zeul ta mika wannan tayi ne a lokacinda ta kai ziyara birnin Damascus.ta kuma amince da bada taimakon kudi da kayan aiki da kudinsu ya kai euro miliyan 34 domin gudanar da aiyukan ci gaba a kasar.Wannan shine karo na farko da kasar Jamus ta mika hannun taimako ga kasar Syria tun bayan kashe tsohon firaministan Lebanon Rafik al Hariri a 2005.